Yayinda take bankwana da majalisar zartaswa ta gwamnatin Shugaba Muhammad Buhari sai da Amina Muhammad tayi kwalla.
Wannan mukami da Amina ta samu ya biyo bayan kashi 75 cikin dari na kasashen Majalisar Dinkin Duniyan da suka yi maraba da surka mata cikin manyan masu gudanarwa a majalisar.
Babban sakataren ya nada Anima Muhammad da wasu mata biyu bisa ga kwarewasrsu da halayensu da yadda suke muamalar diflomasiya da aiki da dan Adam.
Amina Muhammad wadda zata dinga wakiltar Babban Sakataren Majalisar ta fuskar diflomasiya a duniya tace zata yi anfani da matsayinta wajen nisanta musulmi da kin jininsu kan yadda ake alakantasu da aikin ta'adanci.
Tuni dai ta mika ragamar mulkin ma'aikatar muhalli ga karamin ministan Ibrahim Usman Jibrin mutumin jihar Nasarawa.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.