Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farashin Dalar Amurka Ya Fara Saukowa A Najeriya


Harakar canji Dala da Nera
Harakar canji Dala da Nera

Faduwar farashin dalar Amurka a Najeriya ya biyo bayan shigowar harkokin kasuwancin musayar kudi da gwamnatin Najeriya tayi ta hannun Babban Bankin kasar

Gwamnati ta yanke shawarar shiga kasuwar musayar kudi ta yin anfani da Babban Banki a karkashin wani tsari inda bankin zai dinga bada dalar Amurka ga bankunan kasuwanci.

Su bankunan an bukacesu su dinga sayar da dalar wa rukunin mutane ukku, wato dalibai dake karatu a kasashen ketare da marasa lafiya masu bukatar zuwa asibitocin kasashen waje da kuma masu halartar taruka da yawon bude ido a kasashen ketare.

Wani da aka tambayeshi batun sabon shirin sai yace an ce za'a fara sayarwa amma ba'a fara ba saidai da alama zasu fara sayarwa din. Yace ko a wurinsu farashin dala ya sauko. Yace idan farashin dala ya sauka duk abubuwa zasu yi sauki a kasuwa.

Saidai cikin irin mutanen da aka lissafa za'a dinga sayarwa dala ba'a ambaci 'yan kasuwa masu zuwa kasashen waje sayo kayan da suke sayarwa a cikin kasar ba. Babu wanda ya san makomansu, ke nan har yanzu akwai sauran magana.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

Facebook Forum

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG