Wasu 'yan Najeriya na cewa salon jagorancin Farfasa Osinbajo ya dara na maigidansa Shugaba Muhammad Buhari lamarin da yanzu yake haddasa muhawara tsakanin jama'a.
Saidai Fadar Shugaban Kasa ta Aso Rock tace bata ji dadin yadda ake kokarin raba kawunan shugabannin biyu ba. Kakakin Fadar Malam Garba Shehu yayi furuci akan lamarin.
Yace gwamnati guda daya ce, wato gwamnatin da Shugaba Buhari ya kafa tun lokacin da ya kama mulki. Kuma har yanzu ita ce ke "cigaba da aiki" inji Malam Garba Shehu.
Shawarar da majalisar ministoci ta bayar akan tattalin arziki bata canza ba a cewar Garba Shehu. Haka kuma ba'a canza ma'aikatan ba.
Wani dan jarida Muhammad Ibrahim shi ya fara wannan kwatantawar. Shi ya farata a kafar sada zumunta ta Facebook. Yana mai cewa "tsakani da Allah mulkin mataimakin shugaban kasa Farfasa Yemi Osinbajo ya fi na Shugaba Muhammad Buhari tasiri ga talaka" inji Muhammad.
Ya cigaba da cewa ziyarar da Mukaddashin ya keyi a sassan kasar Shugaba Buhari bai yi haka ba sai zuwa kasashen waje. Yace amma lokacin da yake neman zabe babu lungun da bai shiga ba. Jihar Kano da ta fi bashi yawan kuri'u har yau bai kai ziyara ba. Amma Farfasa Osinbajo yana zuwa wurare hatta Niger Delta inda yayi magana mai kwantar da hankali.
To amma dan jarida Bashir Yahuza Malumfashi ya mayarwa Muhammad Ibrahim martani yace ko Buhari yana nan ko baya nan abubuwan da suka tsara zasu yi su ne suke faruwa. Duk rawar da Farfasa Osinbajo yake takawa yana yi ne da bazar Muhammad Buhari.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Facebook Forum