Kungiyar Human Right Watch ta bukaci gwamnatin kasar Senegal ta gudanar da bincike kan muzgunawa ‘yan fafatukar kare hakin bil’adama biyu da aka yi, yayin zanga zangar da aka gudanar a Dakar. Kungiyar tace wadansu matasa ‘yan jam’iyar shugaba Abdoulaye Wade sun kaiwa Alioune Tine da kuma Oumar Diallo hari jiya alhamis. Yan hamayya masu zanga zanga sun yi fito na fito da ‘yansanda yayinda suke zanga zangar nuna adawa da yunkurin sake kundin tsarin mulki da ya shafi zaben shugaban kasa. Masu zanga zangar sun ce yin canji a kundin tsarin mulkin zai bada damar sake zaben Mr. Wade. Tine shine babban magatakardan kungiyar kare hakin bil’adama, African Assembly for the Defense of Human Rights, da suke aiki da Diallo. An kwantar da mutanen biyu sakamakon harin da aka kai masu. Kungiyar Human Rights Watch tana kira ga gwamnatin kasar Senegal ta kyale a gudanar da zanga zangar lumana a kuma daina yiwa ‘yan gwaggwarmaya barazana. Jam’iya mai mulki tayi watsi da yunkurinta na yiwa dokar zabe gyara bayan tashin hankalin da aka yi jiya alhamis.
Kungiyar Human Right Watch ta bukaci gwamnatin kasar Senegal ta gudanar da bincike kan muzgunawa ‘yan fafatukar kare hakin bil’adama biyu da aka yi, yayin zanga zangar da aka gudanar a Dakar.