Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Ghana Ya Kira A Gaggauta Samar da Kudin Bai Daya A Kasashen ECOWAS


Taron samar da takardar kudi bai daya a kasashen yammacin Afirka ko ECOWAS
Taron samar da takardar kudi bai daya a kasashen yammacin Afirka ko ECOWAS

Shugabannin kasashen ECOWAS da suke taro a Ghana zasu kwashi kanaki hudu suna yi domin su cimma matsayi daya akan samar da takardar kudi ta bai daya a kasashensu, abun da shugaban Ghana ya ce yau shekaru 20 ke nan ana magana akan abu daya

Taron da shugaban Ghana Nana Akufo Ado mai masaukin baki yake jagoranta ya samu halartar shugabanin Ivory Coast, Nijar, Togo da gwamnaonin bankunan kasashen tare da ministocin kudi.

Shugaba Akufo Ado a jawabinsa ya ce shekaru 20 ke nan da aka soma batun samun takardar kudi bai daya a kasashen yammacin Afirka dake cikin kungiyar ECOWAS. Ya ce babu shakka an fuskanci kalubale akan batun amma tabbas mun dauki aniyar samun kudi na bai daya lamarin da zai taimaka wurin kasuwanci tsakanin kasashen da bunkasa tattalin arzikin yankin.

Shugaba Akufo Ado ya kira shugabannin kasashen da su daidaita alamuransu domin samun takardar kudi bai daya ya tabbata. Baicin samar da kudi bai daya shugaban Ghana ya kira kasashen su amince da kudurorin da suka ba al'ummar yankin walwalar tafiya cikin kasashensu da yin kasuwanci a koina ba tare da wasu sharruda ba.

Dr Dauda Kontagora masanin tattalin arziki da ya halarci taron ya ce tunanen shugabannin kasashen yammacin Afirka ya na kyau, wato a hade daya, a karfafa kasuwanci da cinikayya kana kudadensu su zama bai daya. Injishi idan kudaden suka zama bai daya zai karfafa tattalin arziki domin 'yan kasuwa ba sai sun nemi canji da kudaden waje ba.

Shi ma Malam Suleimanu Mustapha masanin alamuran yau da kullum ya ce nasarar yunkurin zai yi tasiri wa kungiyar ECOWAS. Koda kasashe biyar dake anfani da turancin Ingila suka amince tsakaninsu da yin anfani da kudi bai daya zai taimaka masu matuka.

Saurari rahoton Ribwan Abbas da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG