Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashe 75 Sun Yi Taro A Kuwait Kan Yaki Da Kungiyar ISIS Da Ta'addanci


NIJAR: Ministan Harkokin Wajen Nijar, Ibrahim Yacouba a taron kasashe 75 a Kuwait dake yaki da ta'addanci
NIJAR: Ministan Harkokin Wajen Nijar, Ibrahim Yacouba a taron kasashe 75 a Kuwait dake yaki da ta'addanci

Gudun don kada 'yan kungiyar ISIS da aka fatattaka a kasashen Syria da Iraq bazuwa kasashensu, ya sa kasashen 75 dake yaki da ta'addanci suka taru a Kuwait domin shirya yadda zasu tabbatar da cin nasara akan ta'addanci cikin kasashensu

Jiya aka fara taron ministocin harkokin wajen kasashe 75 a Kuwait dake yaki da kungiyar ISIS ko kungiyoyi masu alaka da ita ko kuma wasu kungiyoyin ta'addancin.

Ministan harkokin wajen kasar Nijar Malam Ibrahim Yacouba na cikin wadanda suka halarci taron. Ya zanta da Muryar Amurka akan lamuran yaki da 'yan kungiyar Boko Haram da ta'addanci a yankin kasashen Sahel.

Kasashen dake fama da ta'addanci a yankin sun hada da Nijar da Najeriya da Mali da Kamaru da Chadi.

A cewar ministan taron na hadin kan kasashe 75 ne. Wadannan kasashen su ne suka hada karfi domin su yaki kungiyar ISIS da kungiyoyin dake alaka da ita ko kuma wasu 'yan ta'addan.

Manufar mahalarta taron shi ne sani inda suke yanzu a yakinsu da ta'addanci, musamman irin nasarorin da suka samu da abubuwan da ya kamata su kiyaye domin kaucewa sake farfado da kungiyoyin 'yan ta'adda.

Inji Ibrahim Yacouba ta'addanci bashi da iyaka. Wadanda suka fito daga Libya su ne suka bazu zuwa Naijar, Najeriya, Mali da dai wasu kasashen. Ya ce duk duniya kowa ya sani 'yan ta'adda daya suke. Basu da addini kuma basu da iyaka.

Ruguza 'yan ta'adda a Libya da Syria ka iya sake jefa kasashen Afirka da wasu cikin wani sabon tashin hankali musamman idan sun gudu zuwa nahiyar. Abun mamaki idan sun shiga Afirka yankin Sahel suka fi zuwa. Yanzu irin wadannan 'yan ta'addan sun kai dubu uku suna yawo a yankin Sahel. Babu yadda za'a ci nasara a kansu idan ba'a murkushe kungiyoyi irinsu Boko Haram da wadanda suke Mali ko Libya ba.

Abdulaziz Toro na da karin bayani a wannan rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:11:51 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG