Jakadun Majalisar Dinkin Duniya na yankin Sahel sun ce mutane kimanin miliyan1.8 ne za su amfana da ayyukan da ke kunshe da wani tsarin samar da ayyuka da suka yi.
Galibin mutanen da ke cikin matsala sun fito ne daga yankunan Diffa da Tilabery, yankunan da suka fi fama da rikicin ta'addanci.
A shirin na Majalisar Dinkin Duniya, yaki da karancin abinci na kan gaba kamar yadda Bintu Jibo shugabar jakadun a Nijar, ta ce.
Ta kara da cewa, baya ga matsalar karancin abinci, shirin zai maida hankali akan cutar tamowa wadda take addabar yara a cikin shirin kiwon lafiya.
Sannan akwai shirin samar da ruwan sha da inganta ilimin yara.
Bayanai na nuni da cewa yawan mutanen davke cikin kangi a bana, ya zarta na 2017 lamarin da Madam Jibo ta ce yana da nasaba da tabartarewar tsaro akan iyakar Burkina Faso da Mali.
Wannan kuma yana shafar jamhuriyar ta Nijar cewarta.
Hukumomin Nijar ta bakin Firai Ministan kasar Birji Rafini yayin kaddamar da tsarin jaddawalin ayyukan jin-kai na Majalisar Dinkin Duniyan, sun bukaci hadin gwuiwa da gwamnati domin tsara fasali daya tilo daga badi.
Saurari rahoton Sule Barma da karin bayani.
Facebook Forum