Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Bankin Raya Kasashen Musulmi Ya Kammala Ziyarar Aiki Na Yini Biyu A Najeriya 


Shugaban Bankin Raya Kasashen Musulmi Ya Kammala Ziyarar Aiki Ta Yini Biyu A Najeriya.
Shugaban Bankin Raya Kasashen Musulmi Ya Kammala Ziyarar Aiki Ta Yini Biyu A Najeriya.

Shugaban bankin raya kasashen Musulmi, wato Islamic Development Bank, Dr. Muhammad Sulaiman Al-Jessar, ya kammala ziyarar aiki ta yini biyu a Najeriya.

KANO, NIGERIA - Wannan ziyara wani bangare ne na rangadin da ya fara a Afrika, inda ya gana da mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo da sauran Jami’an gwamnati.

Shugaban, wanda ya ziyarci biranen Abuja da Kano, ya sanya hannu a kan yajejeniyar hadin gwiwa ta samar da dala miliyan 500 domin aiwatar da wani sabon shirin bunkasa harkokin noma da dangoginsa a kasar.

Shugaban Bankin Raya Kasashen Musulmi Ya Kammala Ziyarar Aiki Ta Yini Biyu A Najeriya
Shugaban Bankin Raya Kasashen Musulmi Ya Kammala Ziyarar Aiki Ta Yini Biyu A Najeriya

A hira da wakilin Muryar Muryar, Dr Mansur Mukhtar, tsohon ministan harkokin kudi na Najeriya, kuma mataimakin shugaban bankin na Islamic Development Bank a yanzu, ya yi karin haske dangane da dalilan ziyarar da kuma abubuwan da suka tattauna da hukumomin kasar ta Najeriya.

Saurari cikakken rahoton da kuma yadda hirar tasu ta kaya da Mahmud Ibrahim Kwari:

Shugaban Bankin Raya Kasashen Musulmi Ya Kammala Ziyarar Aiki Na Yini Biyu A Najeriya .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:44 0:00

XS
SM
MD
LG