Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Yace Zai Saurari Miyagun Rahotanni Akan Abokan Adawarsa


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

‘Yan jam’iyyar Dimokradiyyar Amurka sun nuna damuwarsu bayan da Shugaba Donald Trump ya nuna cewa a shirye yake ya saurari duk wasu miyagun rahotannin batanci, da za’a kawo mishi daga kasashen ketare akan abokansa na adawa, har ma yake cewa yin hakan ba zai zama abu wani abin da za’a iya dauka a matsayin shisshigi a cikin harkokin zaben kasar ba.

“Ina ganin akwai bukatar sauraron irin wannan bayanin, kuma ni ban ga wata illa a hakan ba”, a cewar Trump lokacinda yake hira da wakilan tashar talabijin ta ABC News jiya Laraba.

Shugaban Amurka din ya kara da cewa, “Idan wani ya kira daga wata kasa kamar Norway, alal misali, ya gaya maka cewa yana da wani bayani akan abokan hamyya, ina ganin zanso naji abun da zai fada.”

Da aka tambaye shi ko yanason irin wannan shisshigin a harkokin zabe, sai yace “Ai wannan ba katsalandan bane, ai duk ‘yan majalisu sunayi.”

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG