Kowane lokaci daga yanzu ana sa ran cewa kasar Mexico za ta tura dakarunta zuwa kan iyakarta da kasar Guatemala a yau Laraba, a matsayin daya daga cikin matakan rage yawan ‘yan gudun hijiran da ke ratso Mexico din da niyyar shiga Amurka.
Sakataren Harkokin wajen kasan Mexico, Marcelo Ebrard ya fadawa manema labarai cewa, a yau Laraba ne za’a tura dakaru 6,000 zuwa can kan iyakar Mexico da sauran wurare a kasar.
Ko da yake bai fadi takamaimen lokacin da za su isa ba.
Ebrard ya karanto wata takarda da ya tura wa Majalisar Dattijai ta Mexico, wacce ke dauke da cikakken bayanin yadda aka cimma yerjejeniyar da ta tanadi tsarin mayar da ‘yan gudun hijira Mexico kafin a kammala neman mafakarsu a kasar Amurka.
Facebook Forum