Jami’an kasar Koriya Ta Kudu sun ce Koriya Ta Arewa za ta so tattaunawa da Amurka, duk kuwa da kalaman caccaka na baya-bayan nan daga Koriya Ta Arewar.
Ofishin Shugaban kasar Koriya Ta Kudu ya ce an yi wannan bayanin ne lokacin da Shugaban Koriya Ta Kudu Moon Jae-in ya gana da tawagar Koriya Ta Arewa ta wasan Olympics, inda dukkannin bangarorin su ka amince cewa ya kamata a samu hulda tsakanin Koriyawan, da kuma tsakanin Amurka da Koriya Ta Arewa a lokaci guda.
Tun da farko wani martani daga kafar labaran gwamnatin Koriya Ta Arewa ta KCNA ya ce takunkumin da Amurka ta kakaba ma Koriya Ta Arewa na baya-bayan nan, tamkar kaddamar da yaki ne.
Martanin ya zargi Amurka ta tayar da fitina a yankin ruwan Koriya, sannan ya yi nuni da cewa Koriya Ta Arewa fa na da makaman nukiliya da ka iya tinkarar duk wata barazana daga Amurka.
Facebook Forum