A jiya Litinin shugaba Donald Trump ya ce duk matakan da Amurka ke ‘dauka kan Koriya ta Arewa tun sama da shekaru 20 da suka gabata har zuwa yanzu, hakka bata cimma ruwa ba.
Cikin wani sako da ya kafe ta dandalin Twitter, Trump ya rubuta cewa “Sama da shekaru 25 kasarmu ta kasa cimma burinta kan Koriya ta Arewa, duk kuwa da biliyoyin dalolin da aka kashe amma a wofi. Babu wani abu da yayi aiki.”
Wannan furuci da Trump yayi, alama ce ta cewa zai iya ‘daukar matakin da zai kawo karshen shirin Nukiliyar Koriya ta Arewa, da kuma kawo karshen cece-kucen da ake.
Ranar Asabar din da ta gabata ma Trump ya rubuta wani sako game da wannan batu, inda yake cewa shugabannin Amurka na baya, sun sha yin magana da Koriya ta Arewa, tare da samar da tarin yarjejeniyoyi barkatai da kuma kashe makuden kudade, amma duk babu abin da yayi tasiri, sai keta yarjejeniyar ake tun ma kafin tawadar da aka rubutata ta bushe, an mayar da jami’an Amurka mahaukata. Amma abu daya ne kadai zai yi aiki akan Koriya ta Arewa.”
Sai dai kuma babu tabbacin abin da Trump yake nufi da cewa abu ‘daya ne kadai zai yi aiki.” To amma da alamu kalamansa sun karkata ga amfani da karfin soja, tun bayan da aka ji shi yana cewa Sakataren Harkokin Waje Rex Tillerson yana batawa kansa lokaci ne kawai wajen tattaunawa da shugabannin Koriya ta Arewa.
Trump da shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un sun kwashe makonni suna cacar baki da junansu, inda har shi Trump din yayi barazanar cewa, Amurka zata ruguza Koriya ta Arewa don ta kare kanta ko kawayenta.
Ita kuma Koriya ta Arewa taci gaba da gudanarda gwaje-gwajin makamanta masu linzami da na Nukiliya, ciki har da harba roka ta saman kasar Japan.
Facebook Forum