Wasu manyan jami’an gwamnatin Amurka sun ce, akwai yiwuwar, shugaba Donald Trump, ya cire hannun kasar a yarjeniyar nukiliya da aka kulla da Iran, sannan ya nemi majalisar dokokin kasar ta sabunta wasu takunkumi a kan kasar.
A makon da ke tafe ake sa ran shugaba Trump zai bayyana shirinsa na daukan wannan mataki, a wani jawabi da zai yi, domin a cewar jami’an gwamnatin kasar, matsayar da aka cimma da Iran, ba ta kare wani muradin Amurka.
Sai dai wannan mataki ba wai zai soke matsayar da aka cimma ba ne a shekarar 2015, amma zai sa a maida zancen gaban majalisar dokokin Amurka ne, inda majalisar ke da kwanaki 60 ta yanke shawarar ko a mayar da takunkuman da aka dagewa kasar ta Iran bayan da aka kulla yarjeniyar, ko kuma aksain haka.
Cire hannun Amurka a wannan matsaya da aka cimma, zai iya bude kofar sake yin dubi kan shirin, amma kuma shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce wannan ba zabi ba ne.
A duk kwanaki 90, sai Shugaba Trump ya bayyana ko Iran tana bin matakan da aka gindaya mata a karkashin shirin.
Sai dai a wata ganawa da ya yi da manyan hafsoshin sojin kasar a jiya Alhamis, Trump ya natata matsayarsa cewa Iran ba ta bin ka’idojin da aka gindaya mata.
Facebook Forum