Shugaban Amurka Donald Trump ya fada jiya lahadi cewa, muddin za’a cimma yarjejeniya tsakaninsa ‘yan jamiyyar Democrat, na kyale bakin haure matsa da iyayensu suka shigo da su Amurka tun suna yara su ci gaba da zama kasar, tilas ne yayi garambawul ga tsarin bada katin green card, kuma ya dauki Karin ma’aikatan shige da fice su dubu 10. Da kuma gina Katanga kan iyakar Amurka da Mexico.
A cikin watan jiya ne dai Trump ya bayyana kawo karshen shiri nan da ya baiwa wasu yara da aka shigo dasau Amurka damar ci gabada kasancewa cikin kasar wato DACA shirin da aka samar lokacin mulkin shugaba Obama da ya kare yaran nan da aka shigo dasu Amurka ba ta hanyar data bata dace ba.
Wadannan bayanai suna kunshe ne cikin wasikar da Mr. Trump ya aikewa shugabannin majalisun a jiya Lahadi. Cikin wasu manufofin shirin shige da fice na gwamnatin sun hada harda da fadada hukuncin wasu ayyukan assha da zasu hana baiwa mutum damar shigowa Amurka, ciki ko har da zamowa wata Dan kungiya, da cin zarafin mata, da cin zarafin yara kanana, tuki cikin maye, wadannan laifuffuka zasu kasance cikin abubuwan da mutun zai aikata da zaisa a iya mayar dashi kasar su daga amurka.
Facebook Forum