Shugaban Afrika ta Kudu bakin fata na farko, Nelson Mandela yana bukin cika shekaru 92 da haihuwa yau Lahadi tare da samun taimakon jama’a a duk fadin duniya. Jama’a a Afrika ta Kudu da kuma wadansu sassan duniya sun shirya gudanar da ayyukan taimakon al’umma na tsawon mintoci 67 yau Lahadi domin tunawa da shekaru 67 da Mr. Mandela ya shafe a harkokin siyasa. Tun farko wannan makon MDD ta yi bukin tunawa da ranar Nelson Mandela ta duniya karon farko domin karrama gwarzo siyasa. Mr. Mandela da iyalansa sun yi buki a kadaice a gidanshi dake birnin Johannesburg yau inda wadansu yara 92 da aka dauko daga kauyenshi Mvezo suka raira wakoki.
Shugaban Afrika ta Kudu bakin fata na farko Nelson Mandela ya cika shekaru 92 ha haihuwa yau Lahadi
Shugaban Afrika ta kudu bakin fata na farko Nelson Mandela yayi bukin cika shekaru 92 da haihuwa yau Lahadi tare da samun gagarumin goyon bayan jama’a a duk fadin duniya.