Kungiyar editocin kasar Afirka ta Kudu ta ce za ta dage da duk karfin ta, ta nuna kin yarda da kafa kotun kafofin yada labarai da kuma wasu ayoyin dokar da aka gabatar a cikin shirin dokar kare yada labarai.
Sanarwar kungiyar editocin da aka wallafa lahadi a cikin manya-manyan jaridun kasar, ta ce abubuwan da aka bada shawarar yi za su takura ‘yancin furta albarkacin baki da kuma zirga-zirgar labarai cikin ‘yanci a Afirka ta Kudu.
Jam’iyyar ANC mai mulkin kasar na tattauna maganar kafa kotun kafofin yada labarai, wadda za ta rika sauraren korafe-korafe game da zargin bada labarin karya, kuma na son rai.
Majalisar dokokin kasar na duba yiwuwar gabatar da shirin dokar kare labarai, wadda kafofin yada labarai su ka ce zai yi tarnaki ga ‘yan jaridar da su ka kware a fannin yin cikakken binciken kwakwaf.
Manyan jam’iyyar ANC na sukar lamirin ‘yan jaridar Afirka ta Kudu bisa zargin su da bayar da labaran da ba haka ba da kuma abun da su ka kira rashin da’ar aikin yada labarai. Masu sukar lamiri sun ce idan aka zartas da dokar, jam’iyyar za ta sake jefa kasar cikin irin yanayin da aka yi fama da shi a zamanin mulkin wariyar launin fata.