An saki ‘yan jaridar nan hudu bayan mako guda da yin garkuwa da su a Najeriya, sai dai kawo yanzu babu cikakken bayani dangane da yanayin sakinsu. Tun farko wadanda suka yi garkuwa da su sun nemi a biya su dala miliyan daya kudin fansa bayan sun sace ‘yan jaridar a jihar Abia dake kudancin kasar ranar Lahadi da ta gabata. Kungiyar ‘yan jaridu ta kasa da kasa Reporters Without Borders ta bayyana sunayen wadanda aka sace da suka hada da Wahab Obba shugaban kungiyar ‘yan jarida reshen jihar Lagos, da Adolphus Okonkwo dake aiki da Radio Nigeria da Sylvester Okere wanda ke aiki da jaridar Champion sai kuma Sola Oyeyipo wanda shima yake da zama a birnin Ikko. Garkuwa da jama’a ya zama ruwan dare a kudancin Nigeria, duk da yake ba safai ake sace yan jarida ba sabili da rashin karfin aljihunsu.
An saki ‘yan jaridar nan hudu bayan mako guda da yin garkuwa das u a Najeriya sai dai ba a bayyana yanayin sakinsu ba.