Masana kimiyya anan Amurka sun sake fasalin halittar sauro ta yadda ba zai iya dauka da yada cutar malariya ga bil’adama ba.
Masana kimiyya a jami’ar Arizona sun bullo da wata halitta dake iya shafar hanjin sauro ta yadda ba zai iya daukar kwayoyi da ke haddasa cutar zazzabin cizon sauro ba.
An wallafa binciken ne a mujallar dakunan bitar kimiyyar sarsalar cututtuka masu yaduwa. Masu binciken suna fatan nan gaba za su saki wan nan sabon sauro cikin daji da nufin murkushe na asali masu yada cuta.
Kusan mutane milyan metan da hamsin a duk shekara suke kamuwa da cutar malariya a fadin Duniya.