Kwana daya bayan da Firayim Ministar kasar Hungary Viktor Orban ya sami gagarumar nasara a zaben kasar, karkashin yakin neman zabe da yake kyamar baki, jam'iyyar dake mulkin kasar tace zata nemi a kafa dokokin da zasu hana kungiyoyin farar hula tallafawa 'yan ci rani.
Jami'an jam'iyyardake mulkin kasar da ake kira Fidesz sun ce majalisar dokokin kasar zata fara aiki kan dokoki da za su hana masu rajin kare bakin haure da 'yan ci rani da zarar ta koma bakin aiki a farkon watan Mayu mai zuwa.
Daftarin dokar zata tilastawa kungiyoyin dake taimakawa 'yan ci raninsu sami izini ministocin harkokin cikin gida na kasar su gudanar da aikin su, kana gwamnati zata aza harajin kashi 25 cikin dari kan gudumawar da irin wadannan kungiyoyi suke samu daga kasashen waje.
Facebook Forum