Shugaba Bola Ahmed Tinibu Ya umurci Majalisar kula da tattalin arzikin Najeriya a karkashin jagorancin mataimakinsa Kashim Shettima da ta fito da matakan rage radadin tattalin arziki da al’umma ke fuskanta a sanadiyyar janye tallafin man fetur a kasar.
Shugaban ya bayyana hakan ne bayan ganawa da kamfanoni masu zaman kansu wanda suka yi alwashin bada gudummuwar manyan motoci 100 domin jigilar ma’aikata.
A wata hira da wakilin Muryar Amurka Umar Farouk Musa a Abuja, Alhaji Zarma Mustafa, mataimakin shugaban kungiyar kamfanin mai na IPMAN, ya bayyana cewa su ma kansu suna so su kawo tsare-tsare da zasu kawo sauki ga al’umma kuma za su tabbatar da cewa gidajen mai sun sami man yadda ya kamata kuma a farashin da ya kamata.
Ya kara da cewa suma zasu bai wa gwamnati ta su gudummuwar wajen tabbatar da cewa sun taimaka wa al’umma ta bangaren harkokin yau da kullum da kuma sufuri.
Bayan bada gudummuwar motocin safa safa domin jigalar ma’aikata, nan gaba kuma farashin man zai sauka saboda za a samu wadataccen mai, a cewar Mustapha.
Saurari cikakkiyar hirar cikin sauti: