Jaridar "New Light Myanmar" mallakar gwamnati ta fada yau laraba cewa wata hukumar bincike mai wakilai 7 zata bi sawun wannan gobara wadda jami'an birnin suka ce wata matsalar wutar lantarki ce ta janyo ta.
Wannan gobara ta jiya talata, ta tashi a tsakiyar lokacin da ake ta tashin hankali na nuna kin jinin Musulmi a kasar Burma, inda aka lalata Masallatai da kadarori na Musulmi a birane da dama a yankin tsakiyar kasar.
An ci gaba da daukar matakan tsaro masu yawa yau laraba a kofar wannan Masallaci na Rangoon a yau laraba, inda 'yan sandan kwantar da tarzoma suke ci gaba da yin sintiri a titin da wannan masallaci yake. Hukumomi su na fargabar cewa wannan lamarin yana iya kara rura wutar tashin hankalin addini a wannan kasa inda mafiya yawan al'ummarta masu bin addinin Buddha ne.
Gwamnati ta ce zata bayyana sakamakon wannan bincike a ranar jumma'a.