Babbar jam'iyyar Musulmi kasar UNCa takaice ta tabbatar cewa babu daya daga cikin kujeru data yi takara da zata sami nasara, haka nan wasu musulmi da suka yi takara bisa ga dukkan alamu suma hakar su bata cimma ruwa ba.
Jam'iyyar NLD ta Aung San Suu Kyi, ce ta sami gagarumar nasara a zaben da aka yi ranar Lahadi, amma bata tsaida musulmi ko daya ba, ta mika wuya ga wata kungiya ta 'yan kishin kasa mabiya addinin Budha, wacce take shirin bakanta jam'iyyar a idanun 'yan kasar mabiya addinin Budha wadanda su sune suka fi rinjaye a kasar.
Haka ma jam'iyyar USDP wacce rundunar sojin kasar take marawa baya wacce take fuskantar mummunar faduwa a zaben da aka yi, ita ma bata tsaida dan takara musulmi ba.
Duk da cewa jam'iyyar NLD ta Aung Suu kyi, bata tsaida wani muuslmi ba domin yayi takaraduk da haka goyon bayanda take dashi tsakanin musulman bai ragu ba.
Wata mataimakiyar shugabar jam'iyyar musulma wacce taso tayi takara ta fasa bisa shawarar da jam'iyyar ta bata domin kyamar da ake yiwa musulmin kasar wadanda ake nunawa a zaman bakin haure wadanda suke neman kawar da addinin Budha baki daya.