Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Muhammadu Buhari Yace Watanni Uku Sun Isa Kakkabe kungiyar Boko Haram.


FILE - Nigeria's President Muhammadu Buhari speaks during a news conference after the Summit of Heads of State and Government of The Lake Chad Basin Commission (LCBC) in Abuja, Nigeria, June 11, 2015.
FILE - Nigeria's President Muhammadu Buhari speaks during a news conference after the Summit of Heads of State and Government of The Lake Chad Basin Commission (LCBC) in Abuja, Nigeria, June 11, 2015.

Watanni ukku sunyi yawa wajen yaki da kungiyar boko haram, kamar yadda Kaftin Abdullahi Bakoji Adamu Mai ritaya ya shaidawa mamud Lalo a cikin hirar da suka yi.

Mamud din ya fara tambayar sa ne ko yaya yake ganin waadin kwanaki 90 din da shugaba Muhammadu Buhari ya baiwa rundunar sojan Najeriya ta gama da kungiyar boko haram?

Wannan lamarin ba wani abin mamaki bane domin ni da naji labarin ma sai nayi mamaki, domin ni ina ganin ma ya tsawaita domin kila kasan shi mutum ne mai tausayi ne, mai son rangwami ga jamaa, bai son wahalar dasu sojojin dama sauran Al’umma.

Sai dai da Mamud yace masa yana ganin cewa watanni ukkun sunyi tsawo Kenan? Anan ko ya amsa da cewa ne.

A gaskiya yayi tsawo kwarai da gaske, sabo da wasu dalilai da zan zayyana maka a ayanzu, domin a lokacin da muke Saliyo lokacin mulki shugaba Abacha, sai ya kira Kwamandan mu ana ce masa Manjo Janar Maxell kobe lokacin yana Kanar, yace masa ya bashi awoyi 24 sojojin Najeriya su tabbatar sun kame garin Freetown kuma a kori shugaban kasan nan da yayi wannan tawayen, zaka yi mamaki yau idan ka koma a tarihi ka bincika sai ka taras tun wannan lokacin aka kama birnin Freetown.

Ranar talata ya bada umurnin sai gashi ranar laraba an kama gidan shugaban kasa, kuma abinda zai baka mamaki shine mu a lokacin da aka bada wannan umurnin sojojin Najeriya suna tsallaken ruwa, wanda sai mun tsallaka da jirgi mai saukar ungulu, wanda kuma shi baya iya daukar manya-manyan makamai, sabo da haka dame kake tsammani za a shiga ciki garin Freetown?.

Da kananan makamai wannan bindiga mai jigida wada ake ce wa GPMD, sai kuma wannan bindigar AK47 da kowa ya sani sai kuma waccan SM Riffle din.

To sai dai da Mamud yace masa baya ganin cewa wannan yakin da wanda suka a Saliyo akwai banbanci, domin a Saliyo sun san inda suke son su tafi, wannan kuma na sunkuru ne ba a ganin abokan gaban anan ko sai Kaftin Abdullahi ya amsa da cewa.

Wancan shinma na sunkuru ne, domin me domin cikin gari wata kasa ce ta wasu, kamar ni nan da nake maka maka Magana ai ban san lungu-lungur kasar ko birnin ba, bani da ilmin gaibun sanin cewa ko dan tawaye ya makale akan wanccan benen, ko kuma yana bisa waccan bishiyar ba zan iya ganewa ba, to idan ko haka ne ashe zamu iya kiran sa yakin sunkuru.

Amma da ya tabo masa batun kalamai Shugaban kasar Chadi Idris Debby da ke cewa kar Najeriya ta hau teburin sulhu da yan boko haram fa? anan ko kaftin Abdullahi cewa yayi.

Gaskiya na yadda da raayin shugaban Chadi ina da wannan raayin .

Har wayau Mamud yace masa yana ganin an dauko hanyar kawo karshen wannan yaki da kungiyar ta boko haram? Haka kake jin ba bukatar tattaunawa da su?

Eh! Shi ban san manufar sa ba gaskiya amma ni musali a manufa ta anan na cewa kar ahau teburin tattaunawa dasu domin gaskiya ta ALLAH wadannan mutanen sun cutar da al’umma, da kasa baki daya har na tsawon shekaru, suna cutar da mutane don haka ni anawa ganin bai dace ace anyi wani sulhu dasu ba, a gani ba wata maana sulhu dasu.

Ga Cikakkiyar hirar tasu

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG