Kungiyar lauyoyi ta najeriya reshen jihar Kano tace zata dauki matakan ladaftarwa akan lauyan tsahon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso Barrister Okechukwu Nweaze sakamakon nuna dabi’ar wuce gona da iri a gaban kotu.
Sai dai kotun tace duk wani mataki da zata dauka ya dogara ne da hujjar data samu daga kotun.
Babbar kotun Kano ce ta yanke hukumcin cewa, kungiyar ta ladabtar da lauyan saboda shishshigin da ya nuna a gabanta yayinda yake kokarin kare tsohon gwamnan jihar Rabi’u Musa Kwankwaso game da karar da aka ce tsohon gwamnan ya shigar, yana neman kotun ta dakatar da duk wani yunkuri da hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC zata yi na kama shi, biyo bayan korafin da kungiyar ‘yan fensho ta jihar Kano ta gabatarwa EFCC cewa, tsohon gwamnan yayi rubda da ciki da biliyoyin naira mallakar ‘yan fansho.
Yayinda yake kokarin kare tsohon gwamnan a gaban kotun, Barrister Okechukwu Nweaze, ya nemi kotun ta hana EFCC wancan yunkuri nata na kama tsohon gwamnan, yana mai cewa, hukumar na kokarin keta alfarmar tsohon gwamnan a matsayin na dan majalisar dattawan Najeriya.
Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko daga Kano