Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Uwa da Abokan Arzikin Mutane Akayi wa Kisan Mummuke sun Bayyana a Tashan Motoci.


Nigeria Boko Haram
Nigeria Boko Haram

Yan uwa da aboka arziki ne suka yi tutruruwa zuwa tashoshin mota domin binciken halin da yan uwan su da suka yi tafiya suke ciki, bayan da wasu mahara suka tare motocin dake kan hanya, ciki ko har da Adamawa Mass Transit a kauyen Du wanda ke kusa da barikin Ladi inda aka kashe direbobi da kuma fasinjoji kamar yadda wannan direban da ya tsallake rijiya da baya ke cewa.

‘’Ko wace mota ke zuwa anan kusa da barikin ladi dama sun dade suna aikata wanna taasar, sai suka tsare mutanen ina ganin duk su kashe mutanen a cikin motar.’’

Su dai yan uwan wasu da suka ziyarci tashoshin motadomin binciken halin da yan uwan su keciki domin ko tun a ranar Littini ne abin ne ya faru.Ga wata baiwa ALLAHda abinda take cewa.

‘’Munzo nan tasha ne domin bincikawa ko yan uwan mu na cikin wadanda aka kashe ne bamu sani ba, shine ya kawo mu tashan nan’’

Sai dai da Ibrahim AbdulAzeez ya tambaye ta kome take son ayi yanzu, sai tace tana so ne a bincika, a san me ke tafiya, shima wannan bawan ALLAH ga abinda yake shaidawa Ibrahim na dalilin zuwan sa tasha.

‘’Munzo duba yan uwan mu domin hankalin mu a tashe domin gaskiya anje a dubo wasu yan uwan mu domin bamu ga wasu daga cikin sub a, a taimaka da a taya mu, asa muna hankali, wadanda muka dawo muka samu a taya mu a dubo muna sauran, haka kuma zamu je neman sauran’’

Kome shugabannin kanfanonin sufuri ke cewa game da wannan batu?

Ga Ibrahim Abdul Azeez da cikaken rahoto

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG