Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Abdulrasheed Maina Ya Yanke Jiki Ya Fadi a Kotu


Abdulrasheed Maina
Abdulrasheed Maina

Tsohon shugaban hukumar fansho a Najeriya Abdulrasheed Maina da ake tuhuma da wawure biliyoyin kudade, ya yanke jiki ya fadi yayin da kotu ke sauraren kararsa a Abuja.

Kafafen yada labaran Najeriya sun ruwaito cewa, Maina ya yanke jiki ya fadi ne a cikin dakin kotun ta tarayya a daidai lokacin da lauyan da ke kare shi yake jawabi.

“Tsohon shugaban hukumar ta fansho ya yanke jiki ne ya fadi, a daidai lokacin da lauyansa, Anayo Adibe yake gabatar da jawabinsa a gaban kotu.” In ji gidan talbijin din Channels.

Kotun dai ta dakatar da sauraren karar bayan da Maina ya fadi don bai wa jami’an tsaro damar su kula da shi.

Rashin lafiyar Maina na daga cikin dalilan da suka sa wannan shari’a ta-ki-ci-ta-ki-cinyewa.

A ranar Laraba hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya, ta kammala jawabinta kan karar bayan da ta gabatar da shaidu tara a cewar jaridar Premium Times.

Sau biyu Maina yana tserewa bayan da aka ba da belinsa, inda a baya-bayan nan aka tiso keyarsa daga Jamhuriyar Nijar.

Ana dai tuhumar Maina ne da laifuka 12 da suka danganci halarta kudaden haram.

Wata shaida da ta gurfana a gaban kotun a ranar Laraba cewa ta yi ikrarin cewa Maina ya taba sayen gida na dala miliyan 3.4 kudu hannu a Abuja.

A halin da ake ciki kotun ta dage sauraren karar zuwa ranar 21-22 na watan Disamba.

XS
SM
MD
LG