Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Jihar Niger Ya Ce Zasu Yi Binciken Kwakwab Domin Gano Abinda Ya Haddasa Kisan Sojoji 12 A Jihar


Gwamnan jihar Niger Alhaji Abubakar Sani Bello, yace gwamnatin jihar zata yi duk abin da ya wajaba domin binciko gaskiyar lamari game da kisan sojoji goma sha daya da wasu fararen hula da aka yi a jihar cikin makon da ya gabata.

A wata zanatawa da amanema labarai a barikin sojoji na Mina bayan da sojojin suka nuna masa wasu tarin makamai da suka ce sun samo su ne a yankin da lamarin ya faru, gwamnan ya ce hankalin sa yayi matukar tashi akan lamarin.

Gwamnan ya bayyana cewa duk da cewa makamai ne da aka kera a nan gida Najeriya, barnar su dai dai take da irin wadanda aka kera a kasashen ketare. Ya kuma kara da cewa wannan alama ce ta nuna cewa yakamata gwamnati ta dauki mataki domin tabbas jama’a nada makamai.

Daga karshe ya bayyana cewa zasu dauki mataki domin tabbatar da dalilan da suka jawo wannan rikici da kuma wanzar da zaman lafiya a daukacin jihar.

Rundunar ‘yan sandan jihar Niger ta ce ta gano bindigogi guda bakwai na sojojin da aka ce sun bace a lokacin da lamarin ya faru, da kuma gawar soja guda a cewar kakain ‘yan sandan jihar DSP Bala Elkana.

Yanzu haka dai rundunar ‘yan sandar jihar ta bada wa’adin mako biyu daga talatar data gabata ga duk wanda ya mallaki bindiga ko wani makami ba bisa ka’ida ba, ya mika shi ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da shi.

Ga Mustapha Nasiru Batsari da Karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG