Wannan shine karo na farko da Shugaba Goodluck Jonathan, zai kai ziyara a jihar Sokoto, tun somawar takkadama tsakaninsa da gwamnan jihar, Aliyu Magatakarda Wammako, wanda daga bisani ya bar jam’iyyar PDP ya koma jam’iyyar adawa ta APC.
Magoya bayan Baffarawan sunce shugaban kasar zai kai ziyarar ne bisa gayyatarsu, inji Hakibu Dalhatu, tsohon mai baiwa tsohon Gwamna Attahiru Baffarawa shawara akan lamuran matasa da dalibai.
Mallam Hakibu yace “Baffarawa ba karamin mutum bane a siyasar Najeriya, don haka a ce shi da magoya bayansa na jihar Sokoto zasu shiga jam’iyya, karbarshi sai babban mutum irin shugaban kasa.”
“Babban tasirin da zuwan zai yi shine shugaban kasa zai zo Sokoto, jama’ar Sokoto sun bukaci yazo ya ganin ma idonsa”, a cewar Mr. Dalhatu.
To sai dai kuma bangaren jam’iyyar APC a jihar, na cewa ko a jikinsu, basa jin ziyarar zata yi wani tasiri. Barrister Inuwa Abdulkadir shine shugaban rikon kwarya na jam’iyyar APC a jihar Sokoto.
“Muna maraba da shugaban Kasa, da zai bar aikinshi mai muhimmanci ya karbi tsohon gwamnan jihar Sokoto a jam’iyyar PDP. Wannan zai kara tabbatar da abubuwan da muka fadi a baya game da shi Shugaba Jonathan, bai ga wani abu mai muhimmanci ba a jihar Sokoto, sai zuwa tashi bukata ta amsar tsohon gwamna na jihar Sokoto, wanda aka siya, aka biya domin a yaki Arewa”, in ji Inuwa Abdulkadir.
Yanzu haka dai, ana kammala shirye-shiryen tarbar shugaban kasa Asabar dinnan, yayinda tuni an soma tsaurara tsaro a wasu sassan na birnin Sokoto.