A wani yunkuri da gwamnati mai barin gado ta Najeriya ta yi na sake yin wasu gyare gyare a kundin tsarin mulkin kasar kwanakin da suka gabata, lamarin na neman zama abin kace nace.
Rahotanni sun nuna cewar shirin na yin wasu canje canje a kundin tsarin mulkin kasar ya ci tura ne a yayin da shugaba Goodluck Jonathan ya ki yarda ya sa hannu akan cigaban shirin wannda ‘yan majilisun tarayya suka mika masa.
A wata hira da ma’aikacin sashin Hausa Usman Kabara yayi da wani lauya mai suna barrister Suleman Lere, yayi Karin bayani a game da lamarin da kuma yadda yake a rubuce a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya kamar haka;
“Idan majalisar kasa tayi tanajin doka, sai ta turawa shugaban kasa domin ya rattaba hannu kamin ta zama dokar kasa. Dokar tace a bashi kwanaki talatin yayi shawara, idan wata kama ta kasance wadda ta hana shi sa hannu, doka tace majalisa ta kira wanna tanaji ta sa mashi hannu daga nan ya zama doka.”
Daga karshe yayi Karin bayani a game da illar rashin sa hannun ga sabuwar gwamnati wanda a cewar sa, rauni ne ga ‘yan majalisar kasa.