Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Donald Trump ya hana fitar da kasidar da 'yan jam'iyar Democrat suka rubuta


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Jam'iyar Democrat ta rubuta nata rahoton kan binciken da ake gudanarwa da ya shafi katsalandan a zaben shugaban kasa na shekara ta dubu biyu da goma sha shida da ake zargin Rasha da yi, sai dai shugaba Donald Trump ya taka masu birki ya hana fitar da shi.

Shugaban Amurka Donald Trump ya hana fitar da kasidar da 'yan jam'iyar Democrat suka rubuta da ta banbanta da bayanan kasidar da jam'iyar Republican ta rubuta tana zargin hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI da yin ba daidai ba a binciken da ta gudanar da ya shafi katsalandan da ake zargin Rasha da yi a zaben shugaban kasa na shekara ta dubu biyu da goma sha shida.

A cikin wasikar da aka fitar jiya Jumma'a. Lauyan fadar White House Don MCGahn yace Trump ya tsaida shawara cewa ba zai bada izinin fitar da kasidar ta jam'iyar Democrat ba, "saibili da takardar ta kunshi bayanan sirri da dama musamman wadansu sassa da bai kamata a fitar a bainin jama'a ba.

A cikin wasikar da aka rubuta ga shugaban kwamitin tattara bayanai na majalisar Devin Nunes an bukaci yin gyara a kasidar kafin a fitar da ita.

Makon da ya gabatar shugaba Trump ya bada izinin fitar da irin wannan kasidar da jam'iyar Republican ta rubuta, inda tayi zargin hukumar FBI da karbar takardar sammaci ba bisa ka'ida ba, ta sawa Carter Page ido, wani tsohon mai ba ofishin yakin neman zaben shugaba Trump shawarwari, kan dangantakarsa da Rasha.

A halin da ake ciki kuma, Fadar White House ta tabbatar jiya da yamma cewa wani ma'aikacinta na biyu ya ajiye aiki bisa zarginsa da cin zarafi a cikin gida.

Kakakin fadar White House Raj Shah yace mai rubuta jawabai David Sorenson ya yi murabus jiya jumma'a. Kwanaki biyu da suke shige, wani babban ma'aikacin Fadar White House Rob Porter ya sauka daga mukaminsa bayanda tsofaffin matansa suka yi zargin cewa ya ci zarafinsu.

Sorensen ya musanta zargin da jaridar Washington Post ta fara bugawa jiya. Tsohuwar matar Sorenson ta shaidawa jaridar cewa, ya rika tada mata da hankali da kuma gallaza mata a lokacin da suke auren da basu jima ba suka rabu.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG