Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Kidaya Kuri'un Zaben Shugaban Kasar Guinea-Bissau


An soma kidayar kuri’un zaben shugaban kasa a kasar Guinea-Bisau, kasar da ta kasa samun kwanciyar hankalin siyasa, tun sa’adda ta sami ‘yancin kai daga kasar Portugal, shekaru 45 da suka gabata.

Shugaban kasar Jose Mario Vaz na neman ta zarce a wa’adin mulki na 2 na tsawon shekaru 5.

Shine kadai shugaban kasar da ya sami kammala wa’adin mulkin sa ba tare da juyin mulki ko an kashe shi ba tun samun ‘yancin kai.

Babban abokin hamayyarsa shine tsohon Firaiminista Simeos Pereira. Dukkan ‘yan takarar 2 sun yi alkawarin amincewa da sakamakon zaben. Wasu ‘yan takara 10 ne ke fafatawa da su a zaben.

Pereira na cikin Firaiminista 6 da Vax ya kora a lokacin mulkinsa. Ya kori Firaiminista Aristides Gomes a karshen watan Oktoba ya sanya wani sabo, to amma Gomes yaki ya sauka daga mukamin nasa.

Kungiyar raya tattalin arzikin Afrika ta yamma (wato ECOWAS) ta sa baki domin kare kasar daga fadawa tashin hankali.

Sai dai duk wanda ya kasance shugaban kasa na gaba, zai fuskanci kalubale da dama, a daya daga cikin kasashe masu karamin karfi a duniya, tare kuma da fatara, cin hanci da rashawa, safarar miyagun kwayoyi, da kuma kalubale na inganta sha’anin kiwon lafiya da ilimi.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG