Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guinea Bissau: Gidajen Rediyo Sun Yi Zanga-zanga


'Yan jarida na zanga zanga a harabar gidan Rediyon Capital FM a Guinea Bissau.
'Yan jarida na zanga zanga a harabar gidan Rediyon Capital FM a Guinea Bissau.

Yawancin gidajen rediyon a kasar Guinea Bissau sun yi shiru na tsawon sa’o’i ashirin da hudu (24) a jiya Alkhamis, domin nuna goyon bayansu bayan da aka kai wani hari a gidan Rediyon CAPITAL FM.

Mataimakin Darektan digan rediyon Sabino Santos, ya sanar da Sashen Portugal (Portugese) na MURYAR AMURKA cewa, a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabatan nan ne da asuba, wasu mutane sanye da rigunan sarki na ‘yan sanda kuma dauke da manyan makamai na zamani suka shiga ofishin gidan rediyon na CAPITAL FM dake babban birnin kasar Bissau da hari.

Ya ce sun lalata na’urorin gidan rediyon; kama daga na’urar dake harba shirye-shirye da ma na’urori masu kwakwalwa gaba daya. Kasancewar sun yada labaran ta kafar facebook.

Dayake gidan rediyon mallakin wani ne, ya na kawance da MURYAR AMURKA, kafar yada labaran kasa da kasa wacce take samun kudaden gudanarwarta daga majalisar dokokin tarayyar Amurka wacce take da ‘yancin yada labaranta ba tare da gwamnati ta fada mata yadda za ta yi ba.

”Jiya Alhamis, ‘yan jarida samda da dozen ne suka yi cincirindo a gaban shalkwatar gidan rediyon na CAPITAL FM a babban birnin kasar Bissau, a wani bangare na gangamin da suka kira shi da ZERO TOLERANCE. The

Kungiyar ‘yan jarida da masu fasahar Guinea Bissau da suka shirya gangamin, sun bukaci ayi addu’a ta rana daya.

Gidajen Rediyo 7 da ke mallakin wasu masu zaman kansu da wasu gidajen rediyon al’umma 23 a fadin kasar da ke Afirka ta yamma sun dakatar da yada labarai da duk sauran shirye-shiryensu.

“Nufinmu shi ne mu nuna mahimmancin rawar da kafafen yada labarai suke takawa wajen cigaban kasar nan," abin da babban sakataren kungiyar cinikayyar Dimantino Domingos, ya fadi kenan. Ya kara da cewa "Mun bukaci muyi shiru a yau."

Lopes ya bayyana harin da aka kai wa Capital FM a matsayin mummunar cin zarafi da take ‘yancin magana.

Kungiyar ta bai wa hukumomin Bissau wa'adin ranar Laraba da su amsa kiran daukar nauyin laifi da kuma yin adalci.

‘Yan sanda sun sanar da ‘yan jaridar cewa, suna nan suna bincike, duk da cewa basu fitar da wani bayani ba a dokance, kana har yanzu ba a gano ko su wa suka aikata wannan aikin ba.

Minista Mamadu Serifo Djaquite, na daya daga cikin manyan jami'an gwamnati kasar da sukayi tir da Allah wadai da wannan harin da aka kai wa Capital FM.

Haka nan ma, kungiyoyin kasa-da kasar da tashar ke mu’amala da su guda biyar, da suka hada da ECOWAS, sun yi Allah wadai da wannan aika-aikar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG