Kasafin kudin Najeriya na wannan karon ka iya shan bam-ban da na sauran shekarun da suka gabata, dalili kuwa shine gangar man fetur ta haura zuwa kusan dala sittin.
A watannin da suka gabata, shugaba Muhammadu Buhari, ya yi ta kokawa musamman akan yadda tsagerun Niger-Delta ke fasa bututun mai, koda shike wannan matsala ta kare duk da barazanar da ‘yan tsageran Avengers suka yi ta dawo da kai hare-hare.
Ko mai talakawa ke cewa dangane da kasafin kudin kasar, Mukhtar Sodangi Binanci, talaka ne mai lura da lamurran yau da kullum a Najeriya, ya bayyana cewa wasu dai-daiku ne kadai ke karuwa da manya manyan ayyukan da gwamnati take gudanarwa a Najeriya, domin har yanzu a cewarsa talakawa na cikin wani hali.
A nasa bangaren, masanin tattalin arziki Malam Yusha’u Aliyu, ya bayyan cewa za a ga banbanci a katsafin na bana idan aka kwatantashi da wadanda suka gabata domin dalilai daban daban, kama daga siyasa zuwa yadda aka tsara gabatar da shi da kuma wasu muhimman dalilai.
Domin karin bayani, saurari rahoton Nasiru Adamu El-kaya a nan.
Facebook Forum