Tun kimanin watanni hudu da suka gabata ne kungiyar darikar shi’a ta gurfanar da gwamnatin jihar Kano, da kwamishinan ‘yan sandan jihar da kuma Antoni janar kuma kwamishinan shari’a na jihar ta Kano a gaban babbar kotun tarayya dake jihar, saboda zargin kisa da cin zarafi da jami’an tsaro suka yiwa ‘ya’yan kungiyar yayin da suke tattaki daga Kano zuwa Zaria a shekarar data gabata.
Kungiyar ta fadawa kotu cewa matakin da jami’an tsaro suka dauka a kan ‘ya’yanta, tauye hakkin su ne na gudanar da addinin da suke so, da ‘yancin kai-komo, da kuma ‘yancin kafawa ko shiga kungiyar da suke muradi kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi tanaji.
Barrister Sale Muhammed, shine lauyan kungiyar kuma ya bayyana cewa tunda babu inda suka taka dokar kasa, akwai bukatar gwamnati ta biya su diyyar kudi Naira miliyan 500.
An sami arangama tsakanin ‘yayan kungiyar da Jami’an tsaro ne a watan Maris na shekarar data gabata, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin ‘yan kungiyar yayin da wasu kuma suka jikkata.
Sai dai a zaman kotun na yau litini, Layar gwamnati Barrister Halima Yahuza, ta bayyana cewa kotun bata da hurumin sauraren wannan kara dan haka kamata yayi ta tsame hannun ta.
Alkalin kotun justice J.K, ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 30, ga wannan wata na Nuwamba.
Daga Kano ga rahotan Mahmud.
Facebook Forum