Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda 'Yan Majalisu Ke Sha Da Kyar A Mazabun Su


Tun shekarar 2015 da aka samu sauyin Gwamnati a Najeriya ake jin labarin ature da mutane keyi wa tsofaffin Gwamnoni da 'yan majalisu, an fara samun mayar da, martani akan yadda lamarin ka iya shafar zaben shekarar 2019

Sannu a hankali lamarin na ci gaba da yaduwa a jihohin Neja, da Kano da Bauchi da Katsina da kaduna, kuma dukana su ‘ya’yan jam’iyya APC mai mulki ne rahotanni ke nunin cewa an yiwa tsofaffin gwamnoni da wasu dake ci yanzu bore harda jifa a wuraren taruka.

Yanzu kuma lamarin ya kai kan ‘yan majalisar tarayya dake wakillatar wadannan jihohi, musamman a mazabun Neja ta arewa da Bauchi, ta tsakiya da wasu sassan Kano da Kaduna da kuma jihar katsina.

Abdulhamid Dan Kirko, matashi ne kuma dan jam’iyyar APC, mai mulki ne ya bayyana cewa akwai wasu da dama cikin ‘yan majalisun da basa yin aikin baki ko na fari a majalisar, zaman dumama benci kadai suke yi, basu san abinda ake kira wakilci ba, domin kawai jama’a sun bi umurnin shugaba Muhammadu Buhari aka zabe su.

A bangaren shugabar mata ta jam’iyyar APC, Dr Ramatu Tijjani, ta ce da irin waddannan korafe-korafe ne ake iya gina Demokaradiyya, kuma daga samma har birnin tarayya, SAK za a yi.

A nasa tunanin, Auwal Musa Ramsanjani, shugaban kungiyar kare hakkin dan’adam, ya bayyan cewa sai anyi da gaske a zaben shekara ta 2019, domin bazai yiwu a cigaba da dibar mutanen da basu.

Ga Medina dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG