Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miyetti Allah Tayi Kira Gwamnatocin Benue da Taraba da Su Soke Dokar Hana Kiwo a Fili


Fulani Makiyaya
Fulani Makiyaya

Kawo yanzu jihohin Taraba da Benue ne suka hana kiwo a duk fadin jihohinsu, a cewarsu sun yi hakan ne domin kawo zaman lafiya. Wannan doka bata shafi wuraren da makiyaya suka saya domin yin sana’arsu.

To sai dai kungiyar makiyaya, Miyetti Allah ta Najeriya, ta kira gwamnatocin da su janye dokokin da suka yi na hana kiwo.

Mataimakin shugaban kungiyar Alhaji Useni Yusuf Boso ne ya yi wannan kira a wajen nadin Alhaji Yakubu Bello a matsayin sarkin Fulanin Oke-Ogun a jihar Oyo da aka yi a fadar sarki Iseyin Dr. Adekunle Salawu.

Alhaji Boso ya yi kira ga gwamnatocin biyu su gaggauta soke dokar domin a samu zaman lafiya. Yace suna da rahotannin dake cewa Fulani na ficewa daga Benue zuwa jihar Nasarawa. Dokar bala’i ce ga makiyaya da manoman.

Shi ko sarkin Iseyin kira ya yi ga manoma da makiyaya su zauna lafiya da junansu. Yace baya son fada ko rigima.

Alhaji Yakubu Bello shugaban Fulani na jihar Oyo shi ne aka nada a matsayin sarkin Fulanin Oke-Ogun.

Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG