Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Nema Goyon Bayan Kasashen Duniya Don Magance Ta'addanci


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake neman goyon bayan kasashen duniya kan wasu manyan matsaloli kamar ta'addanci, tayar da kayar baya, kaurar jama'a, da sauyin yanayi, yana mai sake jaddada cewa kalubalen da ke ci gaba na haifar da babbar barazana ga rayuwar bil Adam.

Shugaba Buhari ya kuma bayyana Najeriya a matsayin kasa mai hankoron zaman lafiya kamar Gambiya, Koriya ta Kudu, Slovak, Australia, Bagladesh da Guinea Bissau.

Da yake jawabi jiya a fadar gwamnati, Abuja, yayin karbar wasikun yabo daga wakilan kasashen shida, Shugaban ya bayyana zaman lafiya a matsayin wani abu na yau da kullun tsakanin kasashen bakwai baya ga dangantakar ‘yan uwantaka tsakanin Najeriya da kasashen.

Ya ce: “Baya ga dangantakar‘ yan uwantaka da ke tsakaninmu, abu daya da Najeriya ta hada kai da kasashenku shi ne zaman lafiya. Zaman lafiya bai yin yawa, abin so ne kuma mai mahimmanci ga ci gaba mai dorewa da cimma burin da Majalisar Dinkin Duniya ta sa gaba.

“Don haka ya zama wajibi a gare mu mu duka bangarorin biyu mu yi aiki daban-daban don cimma zaman lafiya mai dorewa".

XS
SM
MD
LG