Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Gudanar da Taron Kwanaki Biyu Akan Tsaro A Maiduguri Jihar Borno


Janar Buratai da sojoji jami'an tsaro
Janar Buratai da sojoji jami'an tsaro

Ofishin mai baiwa shugaban kasar Najeriya shawara akan harkokin tsaro ya shirya taro a Maiduguri, jihar Borno akan inganta tsaro tare da duba sabbin hanyoyin da za'a bi domin dakile matsalar ta'adanci a yankin arewa maso gabas

Taron ya hada da jami'an tsaron soja da na 'yanasanda da jami'an tsaron farin kaya wato DSS da jami'an Civil Defence da hukumomin shige da fice da na Road Safety da kungiyar matasan sa kai da aka sani da Civilian JTF har da ma jami'an gidan yari.

Duk wadannan an tarasu ne domin su bada tasu gudummawa akan hanyoyin da za'a iya bi domin kawo karshen irin ta'adanci da ya addabi yankin arewa maso gabas tare da yadda za'a tallafawa wadanda suka tuba domin kada su koma jidan jiya.

A wurin taron an baiwa mutane daman tofa albarkacin bakinsu walau a rubuce ko kuma ta hanyar yin bayanai. Nan take jama'a da dama suka dinga yin bayanan irin matsalolin da suke fuskanta musamman dangane da irin kananan hare-haren da ake kaiwa mutanen dake kauyuka kuma har yanzu suna faruwa.

Shugaban taron Mr. Julius Dan Asabe Yakubu yace dama dalilin taron ke nan domin a samun gudummawar jama'a domin mahukunta su san abubuwan dake faruwa kana su san matakan da zasu dauka.

Baicin jami'an tsaro akwai sarakunan gargajiya da shugabannin addinai da suka halarci taron. Wani yace matsalar tsaro a kauyuka ta fi karfin gwamnati su kadai. Sun kira sojoji su dinga yin anfani da abun da jama'a ke fada masu akan lamuran dake gudana musamman a kauyuka domin da zara an fita daga birni cikin tafiyar mil biyu ko uku za'a sami 'yan ta'ada.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:12 0:00

Kudurin wasu 'yan Najeriya na sabuwar shekara a fannin lafiya, da wasu sauye-sauyen da suke fatan yi don samun nasara a rayuwarsu
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 1080p

No media source currently available

0:00 5:16 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 1080p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Karo na biyu kenan a Nijar ake gudanar da bukukuwan Kirsimetin karkashin mulkin soja, inda a bara takunkumin ECOWAS ya dakushe farin cikin
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:52 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG