Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nasarar Trump Ba Zata Shafi Taimakon da Amurka Ke Baiwa Najeriya A Yaki da Ta'adanci Ba


Donald Trump da iyalansa
Donald Trump da iyalansa

Biyo bayan lashe zaben shugabancin Amurka da Donald Trump yayi wasu masu sharhi suka fara nazarin abun da zai faru da dimbin taimakon da Amurka ke baiwa Najeriya wajen yaki da ta'adanci da 'yan ta'ada

Manjo Janar Yakubu Usman mai ritaya yace nasarar Trump ba zata shafi rawar da Amurka ke takawa a yaki da ta'adanci a Najeriya ba.

Yace taimakon tsaro ba abu ba ne na mutum daya. Yarjejeniya ce tsakanin kasa da kasa saboda haka duk wanda ya kama ragamar mulkin kasar Amurka zai duba ya ga irin yarjejeniyar dake kasa.

Dangane da yaki da ta'adanci sabon shugaban Amurka ba zai so ya daina cigaba da bada taimako ba idan ba yana son ta'adancin ya dinga yaduwa ba har ya kaiga kasar. Taimakon da Amurka ke bayarwa yana taimaka mata ita ma ta hanyar hana yaduwar ta'adanci zuwa kasarta.

Bisa ga zafin jinin shi Trump ma yana iya kara taimakon domin ya tabbatar an kawar da ta'adanci. Haka ma tsohon sakataren hukumar kogin Kwara Alhaji Ba'abba Abba yace a karkashin shugabancin Donald Trump taimakon yaki da ta'adanci a yankin tafkin Chadi saidai ya karu. Trump ya fada zai yaki ta'adanci.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:12 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG