Shugaba Buhari yayi amfani da damar wajen bayyanawa sakatare Kerry kokarin da gwamnatinsa take a yaki da cin hanci da rashawa, da yunkurin gwamnatinsa na ganin bayan Boko Haram, da kuma tunkarar matsanancin halin zamantakewa a Arewacin kasar.
Kerry yayi alkawarin Amurka zata ci gaba da taimakawa Najeriya a kokarin da take na tunkarara wadannan kalubale. Daga nan ya godewa shugaba Buhari kan kwazonsa da gudunmawar da yake baiwa kasashen kudiya a kokarin ganin an kawar da ta’addanci.
Shugaba Buhari da sakatare Kerry sun kuma tattauna kan tashin hankalin dake faruwa a yankin Niger Delta, inda sakatare Kerry ya baiwa gwamnatin shawarar ci gaba da ganin an shawo kan lamarin.
Daga karshe Kerry, ya fito karara ya nuna cewa Amurka zata ci gaba da taimakawa Najeriya wajen tunkarar batutuwa da suka shafi tsaro da siyasa da kuma matsalar tattalin arziki.