Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisa Ta Shiga Tsakanin Kungiyar Malaman Jami’a Da Gwamnatin Tarayya


Ginin majalisun tarayyar Najeriya
Ginin majalisun tarayyar Najeriya

Majalisar Dattawan Najeriya tace zata shiga tsakanin kungiyar malaman Jami’o’i da bangaren gwamnatin tarayya, kan batun yajin aikin da kungiyar ke shirin tafiya.

Shugaban kungiyar malaman Jami’o’in Najeriya Farfesa Abiodun Ogunyemi, ya nemi ‘ya ‘yan kungiyar da su fara yajin aikin gargadi na mako ‘daya ranar Laraba.

Majalisa zata gayyato kungiyar malaman jami’o’i a wani kokari na shawo kan yawan yajin aiki da suke shiga. Shugaban kwamitin kula da harkar jami’o’i a Majalisar Dattawa Sanata Barau Jibrin, shine ya shaidawa wakiliyar Muryar Amurka Madina Dauda.

Sanata Jibrin yace harkar ilimi itace ginshikin kowacce al’umma idan kuma aka ga cewa za a samu barazana kan tsarin dole ne a dauki matakan da suka kamata domin kawar da ita. Hakan yasa Majalisa ta zauna domin sauraren kudirin, wanda ta yanke shawarar shugaban Majalisa ne zai shiga tsakani wajen kawo sulhu ga bangarorin biyu.

Cikin kudurin da aka gabatar kan wannan batu ga Majalisa akwai bukatar idan aka dai dai ta, Majalisa ta amince da a saka bukatun malaman cikin kasafin kudin shekara mai zuwa ta 2017. Wannan matsala tsakanin malaman jami’a da gwamnati ta samo asali ne tun lokacin tsohuwar gwamnati da ta gabata, amma Majalisar Dattawa ta sha alwashin ganin ta samar da masalaha.

Saurari hira da Sanata Barau Jibrin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:11 0:00

XS
SM
MD
LG