Kamar yadda aka bayyana mai rike da sandar yana bukatar taimako na musamman ne daga kowane mutum ya hadu dashi.
Idan an gansu suna rike da farar sanda to kamata yayi a tsaya su wuce. Idan kuma ta kama a taimakesu ketare hanya ko kaucewa wani wurin da zai kawo masu wani hadari ko cikas sai a taimaka masu.
Ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe rana ce da makafi kan mika sakonni ga gwamnatoci dangane da irin halin da suke ciki, tare da bayyana matasalolin da suke fuskanta.
Malam Iliya Adamu mai kula da harkokin da suka shafi makafi a shiyar arewa maso gabas ya bayyana irin kokensu musamman su da suka fito daga yankin arewa maso gabas. Yace mafi yawa akan yi magana akan masu gudun hijira amma basa magana akan makasassu musamman ma makafi. Yakamata a san akwai makafi da gudun hijira ya samesu, inji Adamu.
Idan makafi sun samu kansu cikin gudun hijira ba'a kula dasu balantana ma a damu dasu, a cewar Adamu. Ya bukaci a sasu cikin hukumar da ake kokarin kafawa akan nakasassu.
Su ma wasu makafin sun fadi albarkacin bakinsu. Shugaban matasan makafi na arewa maso gabas yace babban matsalarsu ita ce rashin kulawa daga shugabanninsu da gwamnatoci. Misali yace sun goyi bayan barace barace maimakon bada taimakon da zai sa su yi dogaro da kansu. Yakamata a sa yara kanana a makaranta domin a basu ilimin da ya cancanta dasu.
Wata makauniya tace sai ta fita tayi bara kafin ta samu abun da zata ci ta sha, ta sayi sabulun wanki ko na wanka.
A jawabin da gwamnan jihar Bauchi Barrister M.A. Abubakar yayi ya ba makafin tabbacin duba koke-koken da suka gabatar masa. Yace ranar farin ciki ce gareshi. Dangane da koke-koke guda takwas da suka ba gwamnan yace zai zauna da shugabanninsu zasu yi shawara. Ya nemi su bashi mutum guda da zai nada mataimakinsa akan harkokin makafi.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.