A cewar Keften Amuga shekaru hamsin da shida ke nan kiristocin arewa ke taka rawa a fannin siyasar kasar ba tare da sanin inda suka dosa ba amma yanzu canji ya zo.
A lokacin kemfen shugaba Buhari yace muddin korostocin arewa suka zabeshi zai nada kirista daga arewa ya zama sakataren gwamnati tarayya. Alkawarin da yayi ke nan, inji Kefene Amuga.
Yace Shugaba Muhamad Buhari ya cika alkawarin da yayi inda ya nada Injiniya David Lawal Babachir a matsayin sakataren gwamnatin tarayya, matsayin da babu wani kiristan arewa ya taba samu. Baicin Babachir Onarebul Yakubu Dogara ya zama kakakin majalisar wakilai ba tare da tsangwama ba daga shugaban kasa kamar yadda aka saba gani can baya.
A cewar wakilin Tangale lailai Shugaba Muhammad Buhari yana son 'yan arewa su zama daya, wato da kirista da muslmi 'yan arewa su zama daya. Yace ba maganar baki ba ce kawai. Sun ga Buhari ya aiwatar da wannan a mulkinsa.
A nashi jawabi mai baiwa shugaba Buhari shawara a harkar siyasa kuma dan kungiyar kiristocin arewa Ayuba Musa Birma yace wani abu mai mahimmanci a mulkin Buhari shi ne shawo kan rikicin ta'adanci da ya addabi arewa maso gabas. Yace canji ya kawo zaman lafiya. Yace shi kansa dan gudun hijira ne da rikicin Boko Haram ya daidaita amma da zuwan gwamnatin Buhari ya koma garinsu da iyalansa.
Sun yiwa shugaba Buhari fatan Allah ya bashi tsawon rai da koshin lafiya. Baicin haka kiristocin arewa suna bayan shugaban dari bisa dari.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.