Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Kungiyar Boko Haram Sun Mika Kansu Ga Sojoji


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Rundunar sojan Najeriya ta Operation Dole ta bayyana wasu ‘yan kungiyar Boko Haram da suka mika kansu a karamar hukumar Bama a jihar Borno.

Cikin mutum bakwai da rundunar sojan ta nunawa manema labarai akwai amir guda biyu, da ta ce ‘ya ‘yan kungiyar Boko Haram ne da suka mika kansu don kashin kansu a wani gari da ake kira Kumshe dake karamar hukumar Bama a jihar Borno.

Mutanen dai sun hada da maza guda hudu da mace gude da kuma kananan yara guda biyu.

Da yake yiwa Muryar Amurka karin haske kwamandan dake kula da shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya, manjo Rogers Nicholas, ya ce mutanen sun kira sunce sun tuba kuma akwai karin mutane dayawa cikin daji da suka tuba.

Kuma sunce sun fara fitowa ne domin tabbatar da ganin cewa ba za a kashe su ba, sannan su koma su fadawa sauran ‘yan uwansu su fito.

Daya daga cikin mutanen da ya bayyana sunansa Husaini Ali Dakta, kuma likita ne dake yin tiyatar cire harsashi jikin mutane, yana kuma taimakawa mata masu haihuwa.

Da suke bayyana irin halin da suka shiga cikin dajin Sambisa, sun nuna wahalar da suke sha kan rashin abincin da zasu ci.

Domin jin cikakken bayani saurari rahotan Haruna Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:26 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG