Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Aikawa Al'ummar Najeriya Sakon Godiya da Fatan Alheri


Shugaba Muhammad Buhari
Shugaba Muhammad Buhari

Daga birnin Landan kasar Birtaniya inda yake karban jinya saboda ciwon kunne, shugaba Buhari ya aikawa al'ummar Najeriya da sakon godiya da yi masa da kasa fatan alheri musamman cikin wannan wata na azumi

Shugaba Buhari yace assalamu alaikun al'ummar Najeriya ni Muhammadu Buhari ina son na yi anfani da wannan dama na mika sakon barka da shan ruwa da fatan Allah ya karbi ibadunmu baki daya.

Shugaban ya cigaba da cewa haka kuma nake kara kira ga jama'a a yi anfani da wannan lokaci mai albarka, watan Ramadan, da Allah ke karbar addu'ar bayinsa, wajen sanya kasa a addu'ar kawo karshen duka matsalolin dake damunta, Ya taimaka mana wajen sauke alkawuran da muka yiwa al'ummar wannan kasa daga mummunan rauni da aka yi mata.

"Ubangiji Allah ya bamu damuna mai albarka domin al'umma su samu abinci cikin sauki" inji Buhari.

Daga karshe yace "Madalla nagode da addu'o'i na fatan alheri"

Ga cikakken bayanin

please wait

No media source currently available

0:00 0:00:51 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG