Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Buhari Ta Kafa Hukumar Samar da Shinkafa da Alkama Cikin Karamin Lokaci


Mataimakin Shugaban Najeriya Farfasa Osinbajo da Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Mataimakin Shugaban Najeriya Farfasa Osinbajo da Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa wata hukuma da ta kira National Rice and Wheat Task Force wadda zata tsara yadda shinkafa da alkama zasu wadatu a kasar cikin dan karamin lokaci.

Mataimakin shugaban kasa Farfasa Yemi Osibajo yace manufarmu ita ce noma ya zama abun da kasar ta dogara a kai. Yace muna kokarin sake tsara tattalin arzikinmu ta yadda zamu samar da ayyukan yi da kuma ciyar da al'ummarmu, inji mataimakin shugaban Najeriya yayinda yake jawabi wurin kaddamar da hukumar a fadar shugaban kasa jiya.

Farfasa Osibajo yace samar ma al'ummar isasshiyar cimka shi ne abun da gwamnatin Buhari ta sa kan gaba. A matakin farko "mun mai da hankali akan shinkafa da alkama, kuma cikin shekara daya zamu nunawa duniya cewa da gaske mu keyi", inji Osinbajo.

Akwai bukatar a yi tsare-tsare da zasu farfado da duk abubuwan dake da nasaba da noma. Saboda haka ga matakan da aka gindiyawa hukumar ta yi aiki dasu ta kuma bi su sau da kafa.

Abu na farko shi ne ta kayyadewa jihohin da zasu shuka shinkafa da alkama adadin abun da zasu shuka da kuma za'a sarafa

Na biyu hukumar ta kayyade taimakon gwamnatin tarayya da jihohin suke bukata don cimma adadin abun da aka dora masu su yi

Na uku hukumar ta gano hanyoyi mafi dacewa da za'a sayar da albarkatun noma da zasu karfafa manoma da masu sarafa kayan gona

Na hudu hukumar ta duba yadda za'a inganta darajar shinkafa da alkama da ake shukawa a kasar

Abu na biyar wajibi ne hukumar ta fadakar da manoma da masu sarafa kayan noma yadda zasu ci moriyar wani sabon lamuni na musamman da babban bankin kasar ya shirya da kuma wasu taimako da manoma ka iya samu

Abu na karshe hukumar ta tsayar da lokacin da za'a cimma muradun samar da isasshen cimaka a kasar.

Yayinda yake mayar da martani shugaban hukumar gwamnan jihar Kebbi Alhaji Atiku Bagudu ya godewa mataimakin shugaban kasa saboda zabosu su yi wannan aiki mai mahimmanci. Yace gibin dake akwai tsakanin manoma da masu sarafa kayan noma dole ne a cikeshi. Don haka wajibi ne hukumomin biyu, wato hukumarsa da wadda take kula da sarafawa su yi aiki tare domin cimma burin kasar.

Cikin hukumar akwai gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar A. Bagudu, da gwamnan Kano Dr. Abdullahi U. Ganduje da David Umahi na jihar Ebonyi. Sauran sun hada da karamin ministan noma Lokpobiri Heineken da shugaban kungiyar masu noma shinkafa Malam Aminu Goronyo da shugaban kungiyar masu noman alkama Sallihu Muhammad.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG