Abun da yakamata kowa ya yi a Najeriya ke nan ya je asibitin gida kafin ya kama hanyar zuwa kasashen waje neman jinya.
Ciwon kunne da ya kama shugaban kasa yana can cikin kunne ne. Ya kan sa mutum ya dinga jin wani kara ko ihu ya sa mutum ya soma jin bashi da karfi tare da jin kamar zai fadi. Yace an ba shugaba Buhari magani amma bai ji dadi ba saboda haka aka turashi kasar waje.
Yace ba kamar wasu ba da sun ji dan ciwo sai su kama hanyar zuwa kasar waje amma shugaban kasa tunda ya hau mulki ko hutu bai je ba balantana zuwa neman magani a asibitin wata kasa a waje. Yayi shekara guda yana aiki ya kamata a ce ya je hutu.
Dr Rilwanu wanda ya yi shekaru 19 yana aiki a asibitin shugaban kasa yace ya san asibitin amma kuma shugabannin kasar basa zuwa saidai a kai gawarwaki irin na Yar'adua da Abiola. Yace shugaba daya ne yake zuwa lokacin da yake kan mulki shi ne Janar Abdulsalami Abubakar. Amma yanzu ana son a gyarashi a sa kayan aikin da babu tare da yin sabbin gine-gine.
Ga karin bayani.