Kasa da mako daya da kafa gwamnati a jihar Nija dake arewa maso tsakiyar Najeriya, baraka ce take neman ta kunno kai dangane da rabon mukamai a cikin sabuwar gwamnati.
Sabon Gwamna Alhaji Abubakar Sani Bello, wanda aka fi sani da inkiyar Abu-Lolo, ya nada Alhaji Shehu Danyaya, a zaman sabon sakataren gwanatin jihar. Wannan mataki bai yiwa wasu 'yayan jama'iyyar dadi ba, domin kuwa suna zargin maimakon a raba mukai shiya shiyya ba'a yi haka.
Honorable Garba Botso, daya daga cikin masu korafi kan wannan nadi, yace a fahimtarsu ganin Gwamna ya fito daga shiyyar (C), mataimakinsa daga shiyyar (A), suna zaton sakataren gwamnati zai fito daga shiyyar (B). Amma sai gashi an dauko sakataren gwamnati ba ma kadai daga shiyyar (C) ba, amma daga karamar hukumar kontagora, karamar hukumar da Gwamna ya fito.
Tsohon shugaban karamar hukumar Chanchaga Alhaji Ahmed Dogara, yace irin wadannan nade nade na rashin adalci suna suka kai jam'iyyar PDP suka baro.
Sai dai shugabannin jam'iyyar ta APC a jihar suka ce Gwamnan yayi dai dai.
Da yake magana, shugaban jam'iyyar APC na jihar Injiniya Mohammed Imam, yace zargin yazo da mamaki, domin a lokacin tsohuwar gwamnatin PDP, Gwamna da sakataren gwamnati duka daga shiyyar (B) suka fito, kuma babu wanda yayi magana.
Sai dai kakakin jam'iyyar APC a jihar Jonathan Vatsa, yace suna neman jama'a suyi hakuri, kuma da zarar sun gane kuskure a duk mataki da gwamnati ta dauka, za'a yi gyara.
Ga karin bayani.