Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Biden Mai Jiran Gado Na Ci Gaba da Zaben Manyan Jami'an Gwamnatinsa


'Yar majalisar wakilai Marcia Fudge
'Yar majalisar wakilai Marcia Fudge

Kafafen yada labaran Amurka sun ce shugaba Joe Biden mai jiran gado zai nada Marcia Fudge, ‘yar majalisar wakilai daga jam’iyyar Democrat a matsayin sakatariyar kula da harkokin samar da gidaje da raya birane.

Biden zai kuma nada Tom Vilsack ya shugabanci ma’aikatar harkokin noma ta Amurka, mukamin da ya taba rikewa tsawon shekara 8 a baya a karkashin gwamnatin shugaba Barack Obama, wanda Biden din ya yi wa mataimaki. Vilsack kuma tsohon gwamna ne a jihar Iowa, daya daga cikin jihohin kasar da ke da muhimmanci a harkokin noma.

Masu goyon bayan Fudge, dadaddiyar ‘yar majalisar wakilai a jihar Ohio, ciki har da James Clyburn dan majalisar wakilai daga jihar South Carolina, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa Biden samun nasarar zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Democrat, sun nemi shugaban mai jiran gado ya nada ta a matsayin sakatariyar harkokin noma, saboda yadda ta maida hankali wajen ganin an rage matsalar yunwa a matsayin ta na mamba a kwamnitin harkokin samar da gidaje da noma a majalisar.

Amma wasu majiyoyi sun ce Biden ya zabeta ne don shugabantar ma’aikatar ta harkokin gidaje da raya birane saboda ta dade ta na kokari a shirin samar da gidaje masu sauki da ababen more rayuwa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG