Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Barack Obama Ya Jaddada Kurudirinsa Na Hana Iran Kera Makaman Nukiliya

Shugaban Amurka Barack Obama a taron kungiyar kare muradun Isra'ila, lahadi 04/03/12
Shugaban Amurka Barack Obama a taron kungiyar kare muradun Isra'ila, lahadi 04/03/12

Shugaban Amurka Barack Obama ya sake jaddada kudurinsa na amfani da dukkan hanyoyi ciki harda karfin soja wajen ganin an hana Iran mallakar makaman Nukiliya.

Shugaban Amurka Barack Obama ya sake jaddada kudurinsa na amfani da dukkan hanyoyi ciki harda karfin soja wajen ganin an hana Iran mallakar makaman Nukiliya.

Duk da haka shugaban ya gayawa kungiyar kare muradun Isra’ila a Amurka jiya lahadi cewa, ya fi sha’awar ganin an warware wan nan rikici ta hanyoyin difilomasiyya.

Shugaba Obama ya gayawa kungiyar da aka fi sani da lakanin AIPAC mai tasiri, cewa tuni “ana surutai masu yawa na cewa za a yi yaki da Iran”, yace Iran ce take amfana da irin wadan nan maganganu, domin hakan yana kara farashin mai, kafarda Iran din ta dogara akai wajen habaka shirin nukiliyarta.

Yace yanzu ba lokaci bane na cika baki, maimakon haka lokaci ne barin matakan matsin lamba da aka dauka kan Iran suyi aiki da kuma tsananta taron dangi da kasa da kasa suke yiwa Iran domin shirin Nukiliyarta.

XS
SM
MD
LG